NEWS: Su wa ye suka fara Sarautar Kano?

Wannan makala ce da muka yi bayan da muka bukaci ku aiko tambayoyinku a kan tarihin masarautar Kano. BBC ta dauki lokaci don samo amsar tambayoyin daga wajen masana tarihi na masarautar Kano:


Masarautar Kano tana cikin manyan masarautu a kasar Hausa a yammacin Afirka.
Tarihi ya nuna tsohuwar masarauta ce da aka kafa shekaru aru-aru tun zamanin jahiliyya kafin zuwan addinin Islama.
Masarautar ta taimaka wajen bunkasa garin Kano da Arewa da ma Najeriya baki daya.
Garin Kano ya kasance cibiyar kasuwanci a yankin arewacin Najeriya da jamhuriyyar Nijar da ke makwabtaka da garin.

Asalin Kalmar 'Kano'

Mutanen da suka fara zama a Kano makera ne da suka tashi daga garin Gaya domin neman kasa mai arzikin tama, wacce za su sarrafa su yi karfe da ita.
Mutanen sun yi dace da samun kasar mai kunshe da sinadarin tama, sannan kuma mai albarkar noma da ruwa da dazuzzuka da za a iya yin farauta.
Wajen ya kuma kasance mai matukar tsaro kasancewar akwai manyan duwatsu da tsaunuka, da mutane za su iya hawa su fake idan an kai musu hari.
Duwatsun su ne dutsen Dala da Goron Dutse da Fanisau da Jigirya da Magwan.
Akwai kuma koguna daban daban da suka kewaye yankin, da suka hada da kogin Jakara, da kuma kogin Kano.
Hakan ya sa mutane da dama suka ringa yin kaura zuwa yankin domin zama.
Daga cikin mutanen da suka fi shahara cikin wadanda suka fara zama a yankin akwai wani jarumin mafarauci da ake cewa Kano, kuma sunansa ne aka sanya wa garin na Kano.
Masanin Tarihi Dakta Tijjani Muhammad Naniya ya ce har kawo yanzu masana ba su kai ga tantance lokacin da aka fara zama a yankin na Kano ba.
Sannan a cewarsa, masana ba su gama tantance mutanen wace Gaya ce suka fara zama a yankin na Kano ba. Ya ce akawai Gaya ta Kano da ta Nijar da kuma ta yankin Sakkwato.
Babu cikakken bayani kan lokacin da aka fara zama a yankin Kano, amma a cewar Dakta Naniya an taba gano wata makera a kusa da dutsen Dala da masana suka ce ta kai shekara 200 bayan Annabi Isa.
Hakan ya sa ake hasashen cewa garin Kano ya kafu kimanin shekaru 400 kafin addinin musulunci. Ma'ana a yanzu birin ya kai shekara kusan 2000 da kafuwa.

Sarautar Kano

A lokacin da aka kafa garin Kano babu wani shugaba guda daya da ya hada kan jama'a a karkashin mulkinsa.
Jama'ar da suke zaune a kauyuka kamar Dala da Goron Dutse da Fanisau da Magwan da Jigirya duk suna karkashin shugabanci ne na mutanen da suke tare da su.
Daga baya ne da garuruwan suka fara bunkasa, sannan dangantaka tsakaninsu ke kara inganta a lokacin ne aka samu shugaba guda daya da ya hada kan mutanen.

Barbushe

Barbushe, wani shahararren mafarauci ne da masana tarihi suka ce shi ne mutum na farko da ya hada kauyukan a karkashin ikonsa a lokaci guda.
Barbushe ne ya kuma kafa shugabancin Kano.
Masana tarihi na cewa Barbushe jika ne na kimanin 15 ga mutumin da ya fi shahara cikin wadanda suka fara zama a garin, kuma aka bai wa birnin sunansa wato Kano.
DaktaTijjani Naniya ya ce masana tarihi sun fi karkata ga cewa Barbushe shi ne mutumin da ya fara hada kauyukan Kano waje daya ta fuskar shugabanci da kuma addini.
"A lokacinsa ne addinin bautar Tsumburbura ya shahara, kuma Barbushe shi ne babban bokan Tsumburbura. Sha'anin addini shi ne babban abin da ya fara hada kan mutanen Kano."
Bayan zamanin Barbushe da kimanin shekara 200 aka samu wasu mutane daga yankin Daura da suka ci Kano da yaki suka kafa sarauta a karkashin Bagauda a shekarar 999.

Sarakunan Kano

Sarkin Kano Usman IIHakkin mallakar hotoZURIAR GIDAN DABO
Image captionSarkin Kano Usman II yana jiran isowar Yarima Edward dan sarauniyar Ingila a ziyarar da ya kai zuwa Kano a 1925.
Masana sun hadu cewa akwai gidaje da dama da suka yi mulkin Kano tun daga 999 zuwa yanzu.
Masanan sun ce tun daga kan Sarki Bagauda dan Bayajidda har kan sarkin Kano na karshe kafin fulani wato Sarki Alwali dukkaninsu daga jini daya suke.
Sai dai an ci gaba da samun sauye-sauye a tsarin shugabancin da kuma rungumar wasu sabbin abubuwa.
Masarautar Kano ta rabu ne zuwa gidaje biyar kamar haka:
  • Gidan Bagauda
  • Gidan Rumfa
  • Gidan Kutumbawa
  • Gidan Ibrahim Dabo
  • Sarakunan Kano
Share:

1 comment:

  1. Câu lạc bộ đăng ký sv388
    (sv388.club) cung cấp tài khoản xem đá gà hoàn toàn miễn phí cho người xem những trận đấu trực tiếp từ các đấu trường mới nhất. đá gà sv388 Rất hân hạnh được phụ vụ Quý khách.

    ReplyDelete